2 Tar 11:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce,

3. “Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra'ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce,

4. ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da 'yan'uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al'amari daga gare ni yake.’ ” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.

5. Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza.

6. Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa,

7. da Bet-zur, da Soko, da Adullam,

8. da Gat, da Maresha, da Zif,

9. da Adorayim, da Lakish, da Azeka,

10. da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu.

11. Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu.

12. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.

2 Tar 11