2. Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.
3. A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce,
4. “Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama'a.
5. A ba da kuɗin a hannun masu lura da ma'aikata waɗanda suke gyaran Haikalin Ubangiji, su kuma su ba waɗanda suke gyaran Haikalin,
6. wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin.
7. Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”
8. Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.