Yehowash Sarkin Isra'ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa.