Gibeyonawa suka amsa suka ce, “Ba zancen azurfa ko zinariya yake tsakaninmu da Saul ko da gidansa ba. Ba kuma wani mutum muke so mu kashe daga cikin Isra'ila ba.”Dawuda kuma ya tambaye su ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”