2 Sam 1:24-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul!Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.

25. “Jarumawa sun fāɗi,An kashe su a bakin dāga.Jonatan na kwance matacce a tuddai.

26. “Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan'uwana Jonatan,Ƙaunatacce kake a gare ni!Ƙaunarka a gare ni abar al'ajabi ce,Ta fi ƙaunar mace.

27. “Jarumawa sun fāɗi,Makamansu ba su da sauran amfani.”

2 Sam 1