1. Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.
2. Ku saki zuciya da mu, ai, ba mu cuci kowa ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu zambaci kowa ba.
3. Ba don in sa muku laifi na faɗi haka ba, don dā ma na gaya muku, abin ƙauna kuke a gare mu ƙwarai, ko a mace ko a raye, ba mu rabuwa.