2 Kor 6:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na'am da alherin Allah a banza.

2. Domin ya ce,“Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa,Na kuma taimake ka a ranar ceto.”Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!

3. Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,

4. Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,

2 Kor 6