7. Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.
8. Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka, ba a ci ɗunguminmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba.
9. Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu a ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba.
10. Kullum muna a cikin hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, domin a bayyana rayuwar Yesu ta gare mu.
11. Wato, muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.