1. Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.
2. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.
3. Ko da bishararmu a rufe take, ai, ga waɗanda suke hanyar hallaka kaɗai take a rufe.