1 Yah 2:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.

18. Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.

19. Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.

20. Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.

21. Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.

22. Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan.

1 Yah 2