1. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci.
2. Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.
3. Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa.
4. Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi.
5. Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa.
6. Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.
7. Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a'a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji.
8. Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa.
9. Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan'uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu.