1 Tim 3:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.

11. Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.

12. Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa 'ya'yansu da sauran iyalinsu da kyau.

1 Tim 3