64. Haka fa, jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa garuruwa duk da makiyayansu.
65. Daga na kabilar Yahuza, da na kabilar Saminu, da na kabilar Biliyaminu kuma aka ba da waɗannan garuruwan da aka ambaci sunayensu ta hanyar kuri'a.
66. Waɗansu daga cikin iyalan 'ya'yan Kohat, maza, sun sami garuruwa na yankinsu daga cikin kabilar Ifraimu.
67. Sai suka ba su waɗannan biranen mafaka, wato Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu duk da makiyayarta, da Gezer tare da makiyayarta,
68. da Yokmeyam duk da makiyayarta, da Bet-horon duk da makiyayarta,
69. da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta.