1 Tar 6:42-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. ɗan Yowa, ɗan Zimma, ɗan Shimai,

43. ɗan Yahat, ɗan Gershon, ɗan Lawi.

44. Etan na zuriyar Merari, shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta uku, asalinsa shi ɗan Kishi ne, ɗan Abdi, ɗan Malluki,

45. ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,

46. ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,

47. ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.

48. Aka sa 'yan'uwansu, Lawiyawa, su yi dukan hidimomi a cikin Haikalin Ubangiji.

49. Amma Haruna da 'ya'yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra'ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta.

50. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, maza, bi da bi, Ele'azara, da Finehas, da Abishuwa,

1 Tar 6