1 Tar 6:16-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.

17. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, Libni da Shimai.

18. 'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.

19. 'Ya'yan Merari, maza kuwa, su ne Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawiyawa bisa ga gidajen kakanninsu.

20. Zuriyar Gershon bi da bi, su ne Libni, da Yahat, da Zimma,

21. da Yowa, da Iddo, da Zera, da Yewaterai.

22. Zuriyar Kohat bi da bi, su ne Izhara, da Kora, da Assir,

23. da Elkana, da Ebiyasaf, da Assir,

24. da Tahat, da Uriyel, da Azariya, da Shawul.

25. 'Ya'yan Elkana, maza, su ne Amasai da Ahimot.

26. Zuriyar Ahimot bi da bi, su ne Elkana, da Zofai, da Nahat,

27. da Eliyab, da Yeroham, da Elkana.

28. 'Ya'yan Sama'ila, maza, su ne Yowel ɗan farinsa, na biyun shi ne Abaija.

29. Zuriyar Merari bi da bi, su ne Mali, da Libni, da Shimai, da Uzza,

30. da Shimeya, da Haggiya, da Asaya.

1 Tar 6