14. da Seraiya, da Yehozadak.
15. Sarki Nebukadnezzar ya kama Yehozadak, ya tafi da shi tare da sauran jama'a zuwa zaman talala, sa'ad da Ubangiji ya ba da su a hannun Nebukadnezzar don su yi zaman talala.
16. 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
17. WaÉ—annan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, Libni da Shimai.