1. Waɗannan su ne 'ya'yan Isra'ila, maza, Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna,
2. da Dan, da Yusufu, da Biliyaminu, da Naftali, da Gad, da Ashiru.
3. 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan'aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi.
4. Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da 'ya'ya maza biyar.
5. 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
6. 'Ya'yan Zera, maza, su ne Zabdi da Etan, da Heman, da Kalkol, da Darda. Su biyar ke nan.
7. Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.
8. Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.
9. 'Ya'yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.
10. Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban 'ya'yan Yahuza.