22. Gama ka mai da jama'ar Isra'ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
23. “Yanzu dai, ya Ubangiji, bari maganar da ka yi wa bawanka da gidansa ta tabbata har abada, ka kuma aikata yadda ka faɗa.
24. Bari sunanka ya kahu, ya ɗaukaka har abada, a riƙa cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna, shi ne Allah na Isra'ilawa.’ Gidan bawanka Dawuda kuma ya kahu a gabanka.
25. Gama kai, ya Allahna, ka riga ka bayyana wa bawanka, cewa za ka sa zuriyata su zama sarakuna, don haka ne, ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a gare ka.
26. Yanzu dai ya Ubangiji, kai Allah ne, ka riga ka yi alkawarin wannan kyakkyawan abu gare ni, bawanka.