21. Wace al'umma ce take a duniyar nan kamar jama'arka, Isra'ila, wadda kai, Allah, ka je ka fanshe ta, ta zama jama'arka, domin ka yi suna ta wurin manyan abubuwa masu banmamaki, kamar yadda ka kori al'ummai a gaban jama'arka, wadda ka fansa daga Masar?
22. Gama ka mai da jama'ar Isra'ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
23. “Yanzu dai, ya Ubangiji, bari maganar da ka yi wa bawanka da gidansa ta tabbata har abada, ka kuma aikata yadda ka faɗa.
24. Bari sunanka ya kahu, ya ɗaukaka har abada, a riƙa cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna, shi ne Allah na Isra'ilawa.’ Gidan bawanka Dawuda kuma ya kahu a gabanka.
25. Gama kai, ya Allahna, ka riga ka bayyana wa bawanka, cewa za ka sa zuriyata su zama sarakuna, don haka ne, ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a gare ka.
26. Yanzu dai ya Ubangiji, kai Allah ne, ka riga ka yi alkawarin wannan kyakkyawan abu gare ni, bawanka.
27. Ina roƙonka, ka sa wa gidan bawanka albarka, domin ya dawwama a gabanka, gama ya Ubangiji, abin da ka sa wa albarka, ya albarkatu ke nan har abada.”