11. Sa'ad da lokacinka ya yi da za ka mutu, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarka, ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza, zan kafa mulkinsa.
12. Shi ne zai gina mini Haikali, zan kafa gadon sarautarsa har abada.
13. Ni zan zama uba a gare shi, shi kuwa ya zama ɗa a gare ni, ba zan kawar masa da madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na kawar da ita daga wanda ya riga ka sarauta.
14. Zan zauna da shi a gidana da mulkina har abada. Gadon sarautarsa kuwa zai kahu har abada.’ ”
15. Natan kuwa ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
16. Sarki Dawuda kuwa ya shiga alfarwa, ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, mene kuma gidana da za ka yi mini haka?
17. Amma wannan ƙanƙanen abu ne a gare ka, ya Allah. Ka kuma yi alkawari, cewa za ka tsawaita kwanakin zuriyar bawanka, ka ɗauke ni kamar ni wani babban mutum ne, ya Ubangiji Allah.
18. Me kuma ni Dawuda zan ƙara ce maka, a kan girman da ka ba bawanka? Gama ka san bawanka.
19. Ya Ubangiji, saboda bawanka ne, da kuma bisa ga yardar ranka, ka aikata wannan babban al'amari, domin ka bayyana waɗannan manyan abubuwa.
20. Ya Ubangiji, ba wani kamarka, ba kuma wani Allah sai kai, bisa ga duk abin da muka ji da kunnuwanmu.
21. Wace al'umma ce take a duniyar nan kamar jama'arka, Isra'ila, wadda kai, Allah, ka je ka fanshe ta, ta zama jama'arka, domin ka yi suna ta wurin manyan abubuwa masu banmamaki, kamar yadda ka kori al'ummai a gaban jama'arka, wadda ka fansa daga Masar?
22. Gama ka mai da jama'ar Isra'ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.