1 Tar 16:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu.

14. Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.

15. Zai cika alkawarinsa har abada,Alkawaransa kuma don dubban zamanai,

16. Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.

17. Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,

18. “Zan ba ka ƙasar Kan'ana,Za ta zama mallakarka.”

19. Jama'ar Ubangiji kima ne,Baƙi ne kuwa a ƙasar.

20. Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,Daga wannan mulki zuwa wancan.

21. Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

22. Ya ce, “Kada ku taɓa bayina, zaɓaɓɓu,Kada ku cuci annabawana!”

23. Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku dukan duniya,Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana.

24. Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al'ummai,Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane,

1 Tar 16