52. “Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama'arka Isra'ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka.
53. Gama ka keɓe su daga sauran dukan al'ummai domin su zama jama'arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa'ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”
54. Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.
55. Ya tsaya, ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, ya ce,
56. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.
57. Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.
58. Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka'idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu.
59. Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama'arka, Isra'ila, ta kowace rana,
60. domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.
61. Ku kuma jama'arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”
62. Sa'an nan sarki Sulemanu, tare da Isra'ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.
63. Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.
64. A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.
65. Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.
66. A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa.