1 Sar 8:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Dukan jama'ar Isra'ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.

3. Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,

4. suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.

5. Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama'ar Isra'ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.

1 Sar 8