16. ‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”
17. Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra'ila ɗaki,
18. amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali,
19. amma duk da haka ba zai gina Haikalin ba, sai ɗansa wanda za a haifa masa shi ne zai gina Haikali domin sunan Ubangiji.
20. Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila.