21. Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
22. Ya dalaye dukan cikin Haikalin da zinariya, ya kuma dalaye bagaden da yake Wuri Mafi Tsarki na can ciki, da zinariya.
23. Ya yi kerubobi guda biyu da itacen zaitun, ya sa su cikin Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
24-25. Dukan kerubobin irinsu ɗaya girmansu kuma ɗaya. Tsawon kowane fiffike na kerub ɗin kamu biyar, wato tsawon daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan fiffike kamu goma ne.
26. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
27. Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.
28. Ya dalaye kerubobin da zinariya.
29. Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.
30. Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.
31. Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka.
32. Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa'an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.
33. Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun.
34. Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir,
35. ya zazzāna ya adanta su da siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya bai ɗaya.
36. Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al'ul.