Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al'ul.