1 Sar 6:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.

2. Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne.

1 Sar 6