1. Nabot Bayezreyele yana da gonar inabi a Yezreyel kusa da fādar Ahab, Sarkin Samariya.
2. Sai Ahab ya yi magana da Nabot ya ce, “Ka ba ni gonar inabinka don in mai da ita lambu, gama gonar tana kusa da gidana, ni kuwa zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta, idan kuma kana so, sai in ba ka tamanin kuɗinta.”
3. Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”