1. Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
2. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya,
3. “Ka tashi daga nan ka nufi wajen gabas, ka ɓuya a rafin Kerit, a gabashin Urdun.
4. Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
5. Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun.
6. Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin.
7. Da aka jima sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.
8. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya.
9. “Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”
10. Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa'ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.”