3. Ki ɗauki malmalar abinci guda goma, da waina, da kurtun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4. Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa.
5. Ubangiji ya ce wa Ahija, “Ga matar Yerobowam tana zuwa don ta tambaye ka abin da zai faru da ɗanta, gama ɗan yana ciwo. To, da haka za ka amsa mata, gama sa'ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam.”
6. Da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin ƙofa, sai ya ce mata, “Ki shigo, matar Yerobowam, me ya sa kike yi kamar ke wata ce dabam? Gama an umarce ni in faɗa miki labari marar daɗi.