Sa,an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.