1 Sam 7:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. A sa'ad da Sama'ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra'ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.

11. Isra'ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.

12. Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.”

1 Sam 7