1. Sa'ad da na zo wurinku, 'yan'uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba.
2. Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye.
3. Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai.
4. Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,