1 Bit 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,

2. don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.

3. Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa,

4. sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.

5. Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu,

1 Bit 3