16. Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.
17. Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
18. Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai.
19. Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.
20. To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.