1 Bit 2:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba,

14. ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a'aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki.

15. Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari.

16. Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.

17. Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

18. Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai.

1 Bit 2